A KARON FARKO YAR YANKIN AREWA TA LASHE SARAUNIYAR KYAU TA NIGERIA
Ranar Juma’ar Da ta gabata ne Dai Akayi Gasar Sarauniyar Kyau Ta Kasar Nigeria A Garin Lagos Dake Kudancin Nigeria Wanda Ya Tara Mata Da Dama Daga Bangarori Da Yawa Na Kasar Kama Daga Kudu Maso Gabashin Kasar Dama Maso Yammaci Dakuma Arewacin Nigeria.
Amma sai Dai Gasar Ta Bada Ta Bada Mamaki Inda Yar Arewacin Nigeria Tayi Nasara Wanda Yazamana Hakan Shine Karona Farko A Cikin Shekara 44 Da Aka Fara Gasar A Nigeria.
Itadai Wadda Ta Lashe Gasar Mai Suna Shafi Garko Takasance Yar Asalin Jihar Kano Sannan Kuma Tanada Shekara Goma Sha Takwas 18 Sannan Kuma Ta Bayyana Wannan Shine Karonta Na Farko A Zuwan Ta Gasar A Tsawon Ta Na Rayiwa.
Mutane Da Dama Daga Arewacin Nigeria Sun sha Zuwa Gasar Amma Kuma Wannan Shine Karo Na Farko Da Yar Asalin Arewacin Nigeria Tayi Nasara A Gasar Wanda Hakanne Yabawa Mutane Mamaki Bisa La’akari Da Yan Arewa Basu Cika Zuwa Gasar Ba.
Ta Bayyana Farin Ciki Sosai Yayi Bata Kyautar Ta Ta Mai Suna Miss Nigeria A Turance Wanda Mata Fiye Da 18 Ne Sukaje Zagayen Karshe Na Gasar Inda Ta Bayyana Cewar Wannan Babbar Nasara Ce A Gareta Da Tazama Ta Farko A Arewacin Nigeria Da Ta Fara Lashe Wannan Gasa Wadda Ta Bayyana Cewar Tana Cike Da Sarkakiya Sosai.
Comments
Post a Comment